Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya gargadi yan Lebanon da cewa kasarsu na iya komawa kamar zirin Gaza, matukar basu tashi tsaye sun kawo karshen kungiyar Hezbullah ba.
A cikin wani jawabi na bidiyo da ya yi da Turanci, Benjamin Netanyahu ya ce idan har kungiyar da ke samun goyon bayan Iran ta ci gaba da yakar Isra’ila, to kuwa Lebanon za ta faÉ—a cikin wani mawuyacin hali na wani dogon yaÆ™i.
Tun da farko mataimakin shugaban Æ™ungiyar Hezbullah Naim Qassem, ya fito fili ya Æ™aryata cewa an karya lagonsu “karfinmu, na nan yadda yake, abun da makiya ke cewa, wai sun rage karfinmu mafarki ne kawai.”


