Fisayo Dele-Bashiru ya zura kwallaye biyu tare da taimakawa Lazio ta lallasa Auronzo da ci 23-0 a wasan sada zumuncin da suka buga.
Dele-Bashiru ya ci kwallo a cikin mintuna 15.
Wannan ne karon farko da dan wasan Najeriya ya buga wa Lazio.
Dan wasan mai shekaru 23 ya hade da Biancolestti daga kungiyar Hatayspor ta Turkiyya mako biyu da suka wuce.
Lazio na da alhakin sanya tafiyar dindindin a bazara mai zuwa.
Ana sa ran kulob din na Seria A zai kara shirye-shiryen tunkarar kakar wasa ta bana tare da karin wasannin sada zumunta.


