Lauyoyi a Ingila da Wales sun tsunduma yajin aikin makonni biyu, kan batun karin albashi da gwamnati ta ki amincewa da shi.
Kungiyar lauyoyin na bukatar a kara musu kudaden gudanar da aiki da kashi daya cikin hudu na albashinsu, sai dai ministar shari’ar Birtaniya Sarah Dines, ta kira matakin da rashin da’a.
Wata jami’a a Queens Counsel, Michelle Heeley, da ke taimakawa lauyoyi a Birtaniya, ta ce ba bu adalci a batun karin albashin.
Ta ce wannna abu ne da yawancin mambobinsu ke magana a kai, inda da an kara kashi 15 na albashin watakil da ba za a soki gwamnati ba.
Ta ce an akara kashi 15 a kan albashin ne kan shari’un da ba ma za a kamalla ba sai 30 ga watan Satumba. In ji BBC.


