Harin da aka kai a wani asibitin Gaza ya janyo ce-ce-ku-ce a duniya inda aka soke wani muhimmin taron da shugaban Amurka Joe Biden ya shirya yi da shugabannin Larabawa ciki har da Mahmud Abbas na Falasɗinawa.
An shirya Biden ya nufi Jordan ne bayan ya gana da firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu inda zai gana da Sarki Abdallah na Jordan da Shugaba Abdul Fattah al-Sisi na Masar da Abbas.
Da yawa daga cikin shugabannin kasashen Larabawa na zargin Isra’ila da aikata laifin yaki.
Shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas, ya bayyana hakan a matsayin kisan kiyashi, yana mai cewa Isra’ila ta ketare iyaka.


