Gwamnatocin ƙasashen Larabawa da suka taimaka wajen shiga tsakani don tabbatar da tsagaita wuta a Gaza sun yi kakkausar suka ga matakin da Isra’ila ta ɗauka na hana kayan agaji shiga zirin Gaza.
Qatar ta ce Isra’ila ta keta yarjejeniyar da aka cimma a watan Janairu ta kuma yi wa dokokin jin ƙai na ƙasa da ƙasa karan-tsaye.
Wakilin BBc ya ce Isra’ila ta ce dole ne ci gaban tsagaita wutar ya ƙunshi sakin mutanen da aka yi garkuwa da su.
An rawaito cewa, tana shirin bai wa Hamas ‘ƴn kwanaki don gabatar da wani sabon tsari da za a amince da shi, ko kuma Isra’ila za ta ci gaba da yaƙi a Gaza.