A ranar Alhamis ne Al-Nassr ta kammala siyan Aymeric Laporte daga Manchester City kan kudi fam miliyan 23.6 a hukumance.
Kungiyar kwallon kafa ta Saudi Pro League ta bayyana hakan a wani sako da ta wallafa ta shafinta na X (tsohon Twitter).
“Sa hannun Aymeric, Ee, Shi Laporte ne,” Al Nassr ya wallafa a shafinsa na Twitter tare da hoton Laporte da ke sanye da rigar kulob din.
Komawar Laporte zuwa Al-Nassr na nufin dan wasan mai shekaru 29 a yanzu zai koma irinsu Cristiano Ronaldo da Sadio Mane a kulob din Saudiyya.
Dan wasan bayan ya yi fama na tsawon mintuna a Manchester City a kakar wasan da ta wuce a karkashin kociyan kungiyar Pep Guardiola.
Ya buga wasanni 12 ne kacal a gasar Premier kuma ba a saka shi a cikin ‘yan wasan da suka doke Newcastle United da ci 1-0 a ranar Asabar da ta gabata.


