Tsohon dan wasan Chelsea, Frank Lampard, yana cikin jerin wadanda aka zaba domin zama sabon kocin kungiyar kwallon kafa ta Canada.
Lampard ba ya aiki tun lokacin bazarar da ta gabata, bayan zaman kocin riko na Blues.
Dan shekaru 45 yana jiran tayin da ya dace ya zo, amma ba a san ko wani aiki a kasashen waje zai burge shi ba.
Kamar yadda jaridar The Telegraph ta ruwaito, kasar Canada ta zabi Lampard a matsayin kociyan da ake ci gaba da neman wanda zai jagoranci kungiyar zuwa gasar cin kofin duniya ta 2026.
Gasa ce babba ga ƙasar da za ta kasance tare da Amurka da Mexico.
A halin yanzu Mauro Biello shine kocin rikon kwarya na Kanada, bayan ya kasance mataimaki ga John Herdman, wanda ya rike aikin daga 2018 zuwa 2023 lokacin da ya yi murabus ya karbi ragamar horar da kungiyar Toronto FC.