Wata babbar kotun jihar Ondo da ke zamanta a Akure, ta umurci majalisar dokokin jihar da ta kafa kwamitin da zai binciki halin da lafiyar gwamna Rotimi Akeredolu ke ciki.
Rahotanni sun bayyana cewa bayan dawowar sa daga hutun jinya a ƙasar Jamus wata shida da suka gabata, gwamnan ya tare a Ibadan babban birnin jihar Oyo domin ci gaba da kula da lafiyarsa.
Wannan ne ya zaburar da al’umma jihar ke neman a gudanar da bincike kan lafiyarsa.
Wakilinmu na Legas Umar Shehu Elleman ya aiko ma na da wannan rahoto.