Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya fasa zuwa taron ƙungiyar ƙasashen renon Ingila ta Commonwealth na 2024 da za a gudanar a tsibirin Samoa, bayan da jirginsa ya samu a matsala a lokacin da ya yada zango a Amurka.
Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar ya ce a lokacin da jirgin ya yada zango a birnin New York na Amurka, wani abu daga waje ya daki jirgin wanda kuma ya lalata gilas ɗin direban jirgin.
Sanarwar ta ce tuni shugaban ƙasar Bola Tinubu ya amince da shirya wata tawagar ministoci, ƙarƙashin jagorancin ministan muhalli, Balarabe Abbas Lawal domin wakiltar Najeriya a taron, yayin da ake ci gaba da gyaran jirgin mataimakin nasa.
An dai fara taron ne ranar 21 ga watan Oktoba, wanda kuma ake sa ran kammala shi ranar 26 ga watan Oktoba a tsibirin da ke tekun Pacific.
Sanarwar ta ce mataimakin shugaban ƙasar Kashim Shettima tare da tawagarsa da ta ƙunshi ministan harkokin waje, Yusuf Maitama Tuggar sun kama hanyar komawa Najeriya daga Amurka.