Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan ta’addan Lakurawa ne, sun kaddamar da hare-haren hadin gwiwa a wasu kauyuka biyar na karamar hukumar Arewa ta jihar Kebbi, inda suka kashe akalla mutane 10 tare da jikkata wasu da dama.
Zagazola Makama, kwararre kan yaki da tada kayar baya da ya mayar da hankali kan yankin tafkin Chadi, ya bayyana hakan a ranar Litinin a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.
Makama ya ce majiyoyin leken asiri sun sanar da shi cewa kauyukan da lamarin ya shafa sun hada da Birnin Debi, Garin Nagoro, da Yar Goru, da Dan Marke, da Tambo.
A cewar rahoton, ‘yan ta’addan sun far wa kauyukan ne da misalin karfe 8:48 na dare. a ranar 9 ga Maris, 2025, inda suka kona gidaje da harbe-harbe ba gaira ba dalili.
Daga cikin wadanda suka mutu har da Garba Maigari (50), yayin da sauran tara da aka kashe har yanzu ba a san ko su waye ba.
“An kai wasu da dama da suka jikkata zuwa Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Birnin Kebbi domin yi musu magani, yayin da aka ajiye gawarwakin wadanda suka mutu domin a tantance su.
“A mayar da martani, an tura sojojin Najeriya, ‘yan sanda da kuma ‘yan banga zuwa yankunan da abin ya shafa, kuma an ce an dawo da zaman lafiya,” in ji Makama.