Wasu da ake zargin mambobin ƙungiyar Lakurawa ne sun kashe mutum 15 a wani mummunan hari da suka kai ƙauyen Kwalajiya da ke ƙaramar hukumar Tangaza a jihar Sokoto.
Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:00 na rana a ranar Talata.
Ana zargin harin martani ne bayan kashe wasu mutum uku daga cikin kungiyar, ciki har da wanda ake zargin shugabansu ne a wani harin da ya ci tura da suka kai a baya a garin.
Ɗaya daga cikin shugaba a yakin da ya nemi a ɓoye sunansa ya shaidawa jaridar Daily Trust cewa maharan sun dira ƙauyen ne a daidai lokacin da jama’a ke cikin masallaci suna sallar Azahar.
“Muna cikin masallaci lokacin da suka kawo hari da yawansu.
“Da zuwansu suka fara harbe-harbe.” inji shi.
Ya ƙara da cewa jami’an tsaro da shugaban ƙaramar hukumar sun ziyarci ƙauyen a ranar Laraba don halartar jana’izar waɗanda aka kashe.
“Wannan shi ne karo na farko da ƴan Lakurawa suka kai hari kai tsaye a garinmu.
“Amma ina ganin martani ne bayan kashe wasu daga cikin su a wani harin da ya faru a baya,” inji shi.
Wani mazaunin yankin da lamarin ya shafa ya ce maharan sun ƙone gonaki da gidaje da dama tare da lalata wata ariya ta sadarwa.