fidelitybank

Laifin Tinubu ne tsadar rayuwar da Arewa ke fama da ita – Dan Bilki Kwamanda

Date:

Wani fitaccen mai sukar siyasa a Kano, Abdulmajid Danbilki Kwamanda, ya zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da yin watsi da Arewa, yana mai cewa manufofinsa sun kara tabarbarewar tattalin arziki a yankin.

A cikin wani faifan bidiyo na TikTok, Danbilki, wanda fitaccen jigo ne a jam’iyyar APC, kuma mai goyon bayan tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya caccaki gwamnatin Tinubu kan yadda take tafiyar da tattalin arziki, musamman tsadar rayuwa.

Ya yi nuni da cewa, farashin kayan masarufi ya yi tashin gwauron zabo, inda ya ce buhun shinkafa da ya kai Naira 26,000 a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, yanzu ana sayar da shi kan Naira 96,000.

Danbilki ya bukaci Tinubu da ya gaggauta tunkarar wadannan kalubalen tattalin arziki kafin zaben 2027, yana mai gargadin cewa tabarbarewar yanayi na iya zubar da amanar jama’a.

Ya kuma caccaki ‘yan siyasar Arewa a gwamnatin Tinubu, inda ya zarge su da fifita bukatun kashin kai fiye da ci gaban yankin.

A cewarsa, duk da kasancewarsu a cikin harkokin gwamnati, sun kasa bayar da shawarwarin manufofin da za su amfani Arewa.

Da yake tunatar da su cewa mulki na wucin gadi ne, ya yi kira ga wadannan jami’an da su ingiza ci gaba mai ma’ana kafin wa’adinsu ya kare.

sani ahmad

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar Ĉ´ansandan jihar Kaduna, sun buĈ™aci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi Ĉ™ungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban Ĉ™aramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp