fidelitybank

Laifin gwamnatin Buhari ne sanadin talauci a ƙasa – Ƙungiyar Gwamnoni

Date:

Kungiyar gwamnonin jihohi ta ƙasa, ta ce, ikirarin da gwamnatin tarayya ta yi a kan cewa, gwamnonin jihohin kasar su ne suke da alhakin karuwar talauci a kasar,  magana ce da ba ta da tushe ballantana makama.

 Kungiyar ta NGF  ta mayar da martani ne kan  kalaman da karamin ministan kudi na kasar Clem Agba ya yi a baya-bayam nan inda  ya zargi gwamnonin  da rashin  daukar matakan inganta rayuwar mazauna karkara.

A maimakon haka ya ce, sun fi ba ayyukan samar da ababan more rayuwa a birane fifiko da yin gine-gine.

 A cewar ministan  kudin  kashi 72 cikin 100  na al’ummar kasar da ke fama kangin talauci na zaune ne a yankunan karkara inda ya yi ikirarin cewa gwamnoni sun yi watsi da su.

Sai dai  Abdul Razak Bello Barkindo wanda shi ne kakakin  kungiyar gwamnonin ta Najeriya ya shaida wa BBC cewa kalaman ministan ya bai wa gwamnonin kasar mamaki.

“ Ba mu zaci cewa shi wannan ministan zai yi furuci irin wannan  ba, dalili kuwa shi ne  ba mu saba ka-ce-na-ce da gwamnatin tarayya ba, sannan kuma bai cancanta ba, saboda gwamnatin tarayya tana da gwamnoni 22 a cikin jam’iyyarta.’’ In ji shi.

Ya kara da cewa, ‘’Idan gwamnatin tarayya tana ganin akwai  abin da ya kasa toh ina ganin irin manufofin jam’iyyar ce  ta kasa., ba su hana su yi abin da ya kamata su yi ba.’’

besda

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An ceto Mutane 25 da syka kife a kwale-kwalen Sokoto

Hukumomi a jihar Sokoto sun ce, sun samu nasarar...

An fara duba rabon gyaran arzikin Najeriya

Shugaban Hukumar rarraba arziƙin ƙasa RMAFC, Mohammed Shehu, ya...

Kwallaye 6 da aka zurawa Santos a raga ta sanya Neymar ya fashe da kuka

Ɗan wasan tawagar Brazil, Neymar ya fice daga cikin...

Hukumar Shari’a ta magantu kan sadakin dubu 20 da ya yamutsa hazo a Kano

Hukumar shari’a ta jihar Kano, ta ce ba a...

Cutar Mashako ta yi ajalin Yara hudu a Kano

Rahotanni na cewa cutar mashaƙo wadda aka fi sani...

Cin zaben da NNPP ta yi a Kano cuwa-cuwa ne – Ata

Ministan Jiha na Gidaje da Cigaban Birane, Rt Hon...

Mutane kusan 40 sun ɓace sakamakon haɗarin kwale-kwale a Sokoto

Aƙalla mutum 40 ne ake nema bayan haɗarin kwale-kwale...

APC ta yi kwaf daya a zaben cike gurbin Kaduna da Jigawa

Jam'iyyar APC mai mulki a jihar Jigawa ta yi...

Ba mu yarda da zaben Ghari da Tsanyawa ba – NNPP

Jam'iyar NNPP mai mulkin jihar Kano a arewacin Najeriya...

QPC ta nemi INEC ta soke zaɓen Kano

Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta nemi hukumar zaɓe...

Zaɓen Kano: An kama Mutane 288 da tayar da zaune tsaye

Rudunar ƴansandan jihar Kano, ta sanar da kama mutum...

An Kama wakilin jam’iyya da Naira miliyan 25.9 na Siyan Kuri’a

Jami’an tsaro sun kama wani da ake zargin wakilin...
X whatsapp