Rundunar tsaro ta kasa, ta yi ƙarin bayani game da sallamar sojan ruwan nan Seaman Abbas Haruna daga aiki.
A wajen wani taron manema labarai da ta kira a Abuja, hedikwatar tsaro ta ce, an sallami Seaman Abbas daga aiki ne bayan wata kotun soji ta same shi da wasu laifi uku da ake zarginsa da aikatawa.
Jami’in hulda da jama’a na kariya ta Najeriya, Birgediya Janar Tukur Gusau, ya shaida wa BBC cewa, Seaman Abbas, ya yi wasu abubuwa na rashin ɗa’a.
Tukur Gusau, ya ce kwamandan bataliya da wannan soja ke aiki ya kasance yana magana da sojojinsa, to sai shi Seaman Abbas ya fara surutu da kuma wasu abubuwa na rashin ɗa, don sakamakon haka sai kwamandan ya ce masa ya kai kansa wani ɗaki da ake tsare mutane idan sun yi laifi, to sai sa hannu zuwa.
“Daga nan ne sai kwamandan ya ce, tun da alamar zuwa a karɓe bindigar dake hannunsa, to maimakon ya aika bindigar sai ya fara harbe-harbe har sai da ya fitar da harsashi 16, to Allah ya kare bai harbi kowa ba”.
Tukur Gusau, ya ce a aikin soja ba a wasa da batun bindiga ko harsashi, domin harsashi idan soja ya fitar sai an bibiya an ga me yasa ka fitar da shi.
Jami’in hulda da jama’a na kariya ta Najeriya, ya ce, “Bisa ga wannan aka tuhume shi inda aka tura shi kotun soja, kuma koda aka kai shi ya amsa laifinsa, a kan haka ne kotu ta tuhume shi da aikata laifuka uku” .
Ya ce a 2023, kotun ta kore shi daga aiki.
Tukur Gusau, ya kuma bayyana cewa a ka’idarsu ta aikin soja dole sai an nuna wannan kayan na kotu an kai wa manyan sojoji na suke yanke kayan Karshe wato kayan ko akasin haka da dokar kotu.
Kuma kafin taba soji su yanke na karshe sai sun nemi ƙarin bayani daga lauyoyi na soja manyan da mai laifi ke aiki.
Jami’in hulda da jama’a na kariya ta Najeriya, ya ce, Da farko sai da Seaman Abbas ya nuna kamar bashi da lafiya, don haka sai da yaje asibiti da dama don a tabbatar da cewa ba’ayi masa shari’a a cikin yanayi na rashin lafiya ba.
Kuma asibitocin sun tabbatar da cewa lafiyarsa ƙalau, sannan ne kuma aka yi masa shari’a.
Kimanin shekaru biyar kenan da aka tuhumi sojan ruwan wato Seaman Abbas Haruna, da aikata wasu lokutan a lokacin da aka tura shi aiki a jihar Taraba.
An dai tabka zazzafar mahawar a sassa sada zumunta na Najeriya game da zargin cin zarafi da kuma karin sojan ruwan bayan da matarsa ta bayyana cewa, an ɗaure shi shekaru shida cikin yanayi har ya samu taɓin hankali.
A cikin wani faifan gidan matar Abbas Haruna, ta bayyana cewa an gana masa azaba ta wuce misali.
Matar mai suna Hussaina ta bayyana ne a wani shiri na gidan kayan na ‘Brekete Family’, inda a ciki ta bayyana wasu zarge-zargen cewa ba a yi wa mijinta da ma su nunasa ɗin adalci ba.
Bidiyon na Hussaina ya karaɗe sassa sada zumunta, inda aka riƙa yaɗa shi, wasu na zagi, wasu na Allah wadai, wasu kuma suna cewa a dai yi musu.
Seaman Abbas Haruna dai ya kwashe shekaru 12 yana aikin soji kamar yadda mai dakin nasa Hussaina ta bayyana cewa “yana cikin sojojin ruwa na 21AK” abin da ke aikin ya fara aikin ne a aikin 2012.


