Rundunar sojan sama ta kasa ta tabbatar cewa, matuƙa jirginta biyu ne suka rasu a hatsarin da jirgin su ya yi a Jihar Kaduna.
Jirgin ya faɗo ne a yammacin jiya Talata a wani sansanin sojan saman kuma duka mutum biyun da ke ciki ne suka rasu.
Rundunar ta bayyana sunan dakarun nata da suna Laftanal Abubakar Muhammed Alkali da Laftanal Elijah Haruna Karatu.
A yau Laraba Hafsan Sojan Sama na Najeriya Air Marshal Oladayo Amao ya kai ziyara wurin da hatsarin ya faru don jajanta wa dangin mutanen.
Kakakin rundunar, Edward Gabkwet, ya ce za su yi “nutsattsen bincike don gano abin da ya haddasa hatsarin”.