Gernot Rohr ya goyi bayan dan kasar sa Bruno Labbadia ya taka rawar gani nan take a Super Eagles.
A ranar Talata ne hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF ta nada Labbadia a matsayin kocin Super Eagles.
Kocin mai shekaru 58, zai kasance Bajamushe na shida da zai jagoranci zakarun Afirka sau uku.
Rohr, wanda ya jagoranci Super Eagles tsakanin 2016 zuwa 2021 ya bayyana Labbadia a matsayin koci na kwarai.
SCORENigeria ya ruwaito kocin mai shekaru 71 da haifuwa ya ce “Shi koci ne mai kyau, ina fatan hukumar NFF da magoya bayan Najeriya sun yi masa kyakkyawar tarba.”
“Yana da gogewa a gasar Bundesliga, ina fatan ya gaggauta samun hanyarsa a Najeriya, wanda yanayi ne na daban.”
Rohr zai kara da Labbadia lokacin da Jamhuriyar Benin za ta kara da Super Eagles a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin Afrika na 2025 a birnin Uyo a ranar Asabar 7 ga watan Satumba.