Fadar gwamnatin Rasha Kremlin ta ce, labarin da ake ta yadawa cewa, an sanya wa attajirin nan dan kasar Roman Abramovich guba a wurin taron neman zaman lafiya a farkon watan nan ba shi da kamshin gaskiya.
Kremlin ta ce labarin “Wani makami ne na yaki”.
Fadar gwamnatin Rasha ta ce, Abramovich bai halarci taron tattaunwar da aka yi a Turkiyya a matsayin wakilinta, ko da yake an dauke shi a hoto tare da jami’an Ukraine.