fidelitybank

Labarin mu na kaiwa Ƴan Bindiga abinci ƙarya ne – Ƴansanda

Date:

Rundunar ƴansandan Najeriya ta musanta rahotannin da ake yaɗawa cewa jirgin sama mai saukar ungulu mallakinta yana kai wa ƴanbindiga abinci a dajin jihar Kogi.

Rundunar ta ce labarin ƙanzon kurege ne da baya da tushe bare makama.

Kakakin rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya ce bidiyon da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta na wani aiki ne da jami’an rundunar suka yi a yankin Obajana na jihar Kogi, kuma an cika duk wata ƙa’ida kafin ƙaddamar da aikin.

Sanarwar da ACP Adejobi ya fitar ta ce “Ba kamar yadda ake yaɗa labarin ƙanzon kurege ba cewa jirgin saman mu yana kai wa ƴanbindiga abinci a cikin daji, bidiyon na wani aikin haɗin gwiwa ne tsakanin ƴansanda da ƴanbanga da mafarauta.”

Rundunar ta ce ta gudanar da aikin ne a ranar Asabar 10 ga watan Mayun 2025 a jihar Kogi.

Ta kuma yi bayanin cewa an shigar da jirgin sama mai saukar ungulun ne a cikin aikin domin tallafawa jami’an rundunar da takwarorin su a aikin su na fatattakar ƴanbindiga.

Rundunar ƴansandan Najeriyan ta yi Allah wadai da masu yaɗa wannan labaran ƙanzon kurege, tare da jaddada aniyarta ta ci gaba da gudanar da aikin ta a cikin ƙwarewa da bin doka.

natforce 
latest news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Fernandes na duba yiwuwar barin Man Utd zuwa Al-Hilal

Bruno Fernandes na duba yiwuwar ficewa daga Manchester United...

Gwamnatin Tinubu ta jefa al’umma fiye da miliyan 150 cikin tsananin talauci – NLC

A daidai lokacin da gwamnatin shugaban Najeriya Bola Ahmed...

Sojoji sun ce sun hallaka ƴan Ta’adda 60 a jihar Borno

Dakarun sojijin Operation Haɗin-Kai sun ce sun kashe ƴan...

Zan cigaba da jajircewa a kan rantsuwar da na yi ta kujera ta – Fubara

Gwamnan jihar Ribas da aka dakatar, Sim Fubara, ya...

Ambaliya ya kashe Mutane a jihar Neja

Wasu rahotanni sun bayyana cewa, mutane da dama sun...

Kotu ta tabbatar da nasarar Gwamnan Edo

Kotun daukaka kara da ke Abuja ta amince da...

An kashe aƙalla mutum 10,217 a mulkin Tinubu – Amnesty

Wani bincike da ƙungiyar Amnesty International ta fitar kwanan...

Gwamnati ba ta tausayin Talaka – Atiku

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaben...

Elon Musk ya ajiye aikin da Trump ya naɗa shi

Hamshaƙin attajirin nan Elon Musk ya sanarda aniyarsa ta...

‘Yar Najeriya ta haihuwa a aikin Hajjin bana

Wata mata da ta je aikin hajji daga jihar...

Rashin nadi da jinkiri ne ya kawo rashin nasarar mu a kakar 2024/2025 – Kano Pillars

Kungiyar Kano Pillars ta yi imanin cewa jinkirin shirye-shiryen...
X whatsapp