Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Mohammed Idris, ya karyata rahoton da ke nuna fargabar juyin mulki a kasar nan.
Ministan ya bayyana rahoton a matsayin karya ba tare da wata shakka ba kuma wani mummunan aiki na rashin gaskiya.
Ya ce rahoton ya fito ne daga wasu masu kin kishin kasa da suke son rusa Najeriya, wanda mugun nufinsu shi ne tada zaune tsaye a kasar nan da kuma zagon kasa ga gwamnatin da ke ci a yanzu.
Idris ya ce gwamnati ba za ta dauke hankali ko razana ba, wajen yin watsi da sauye-sauyen da ake yi da nufin farfado da tattalin arziki da samar da hanyar wadata ga ‘yan kasa.
Ministan ya ci gaba da cewa, a yanzu ta tabbata cewa, wasu mutane da ke cikin halin kaka-ni-kayi, sun koma yada labaran bogi, domin zubar da amanar jama’a ga gwamnati tare da haifar da fitina a kasar nan.
Idris ya ce gwamnati za ta yi amfani da ‘yancinta a cikin dokokin Tarayya, domin dakile ayyukan da ba su dace ba, tare da shawo matsalar tabarbarewar tsaron kasa da kuma dimokuradiyya da kasar ke fama da shi.
Ya bukaci jama’a da su guji yada ko fadada rahoton da ba shi da tushe.