Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta yi rashin nasara a hannun Real Betis a filin wasan ta na Camp Nou a ranar Asabar.
Wannan dais hi ne karo na farko da sabon mai horas da Barcelona, Xavi ya yi rashin nasara a gasar La Liga.
Dan wasan Betis, Juanmi ne ya zura kwallo wanda ya baiwa Real Betis zaman ta 4 da maki 30, yayin da Barcelona ta 7 a tebiri da maki 23.