Hukumar hana fasakwauri ta Najeriya, ta dakatar da sayar da kayan abinci da ta fara sayarwa a kan farashi mai rahusa, sakamakon turmutsitsin da ya yi sanadin salwantar rayuka a hedikwatarta da ke unguwar Yaba a birnin Legas a ranar Juma’ar da ta gabata.
Kakakin hukumar ta Kwastam Abdullahi Maiwada ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.
A ranar 20 ga Fabrairu, 2024 ne Hukumar ta ce za ta sayar da kayan abincin da aka kama a farashi mai rahusa, domin rage wahalhalu da tsadar rayuwa a kasar.
“An fara sayar da kayan abincin a farashi mai rahusa a natse kuma cikin kamala da misalin karfe 0800,” in ji Maiwada
“Mun ji daɗin haɗin kan ɗimbin jama’a da suka haɗa da tsofaffi da nakasassu da mata masu juna biyu, da sauran ’yan Najeriya masu rauni”, inda ya kara da cewa “sayar da kayan abincin ya kasance har zuwa kusan ƙarfe 5 na yamma, kamar yadda sama da masu cin gajiyar 5000 da ‘yan jarida suka tabbatar.”
Sanarwar ta kuma kara da cewa duk da haka, rikici da tashin hankali da ba a taɓa zata ba ya ɓarke a lokacin da muka ce mun rufe sayar da kayan abinci a ranar da cewa za mu ci gaba washegari, wanda ya haifar da sakamako mara daɗi.
“Dandazon mutanen sun kasance cikin zaƙuwa inda suka riƙa ture shingayen da muka gindaya domin neman buhunhunan shinkafa wanda aka samu asarar rayuka da jikkata wasu da dama.” In ji Maiwada.
Hukumar dai ta mika ta’aziyyarta ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a wannan mummunan lamari.