Sabon zababben shugaban kasuwar wayar hannu ta Farm center a jihar Kano, Hassan Ba Wasa, ya bada tabbacin kawo sauyi a kasuwar tare da tabbatar da walwalar ƴan kasuwar da kwastomominsu.
Shugaban kungiyar kasuwar ya bayyana hakan ne a wata sanarwar da a ka rabawa Manema labarai a Kano.
Ya ce, “Nasarar da na samu daga Allah ce, ba kuma dan na fi Kowa ba, Allah ne ya ba ni, domin haka zan tafi da dukkanin ‘ya’yan kungiyar, domin samar da ci gaba a kasuwar ta Farm center”. In ji Hasssn
Sabon zabbaben shugaban ya ce, zai hada kai da sauran abokan takarar sa wajen ganin an samarwa al’ummar kasuwar kyakykyawan yanayin na kasuwanci, tare da yin aiki da masu ruwa da tsaki a Gwamnati da Kamfanoni, domin ganin kwalliya ta biya kudin sabulu.