Hukumar hana fasa ƙwauri reshen jihar Kebbi, ta ce, ta samu nasarar ƙwace wasu abubuwa da aka yi fasa ƙwaurinsu zuwa ƙasar na miliyoyin kuɗi.
Baban kwantirolan hukumar mai lura da jihar, Ben Oramaluga ne ya bayyana haka ranar Asabar a lokacin taron manema labarai a birnin Kebbi.
Ya ce jami’an hukumar sun kama ƙullin tabar wiwi 371, da ƙwayar ‘diazepam’ kwali 98.
Mista Oramaluga ya ƙara da cewa sun kuma kama fatar jakuna 1080, da buhu 37 na shinkafar waje, da dilar kwanjo 16, da man fetur kimanin lita 30 da wata ƙaramar mota kirar Toyota Corolla.
Babban kwantirolan jihar ya ce ƙwayar da suka ƙwace an ƙiyasta kuɗinta ya kai sama da miliyan 90.
Ya ƙara da cewa jami’ansa sun kuma kama wani mutum da suke zargi da hannu a shigar da tabar zuwa ƙasar, inda ya ce za su miƙa shi da ƙwayoyin hannun hukumar NDLEA mai yaƙi da sha da safarar miyagun ƙwayoyi a ƙasar.


