Hukumar Kwastan, Zone ‘A’, Legas, ta ce, ta kama kayan fasa-kwauri da aka kiyasta kudinsu ya kai Naira miliyan 7,116,932,050, tsakanin Janairu zuwa Yuni 2022.
Rundunar ta kuma bayyana cewa, ta kama mutane 103 da ake zargi da yin fasa kwaurin, a daidai wannan lokacin da ake bincike.
Mukaddashin Kwanturola na sashin Ayyuka na Tarayya (FOU), Hessein K. Ejibunu, mataimakin kwanturolan hukumar kwastam DC, ya bayyana hakan a Legas ranar Litinin yayin ganawa da manema labarai.
Ya yabawa jami’an sashin sa; Inda suka ce kwazon da suka yi wajen aikin ya samu gagarumar nasarar da suka samu a cikin watanni shida da suka gabata.