Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun, ya bukaci hukumar kula da shige da fice ta kasa reshen jihar Osun da ta kawar da duk wani bata gari da ta ke yi domin tabbatar da tsaro a jihar.
Gwamna Adeleke ya bayar da wannan umarni ne a ranar Talata a ofishin hukumar shige da fice ta Osun da ke Ilesa.
Adeleke, wanda ya yi nuni da cewa jihar cike take da bakin haure da suke gudanar da aikin hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, ya kara da cewa dole ne a duba ayyukansu.
Da yake mika godiyarsa ga ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola kan kawo ofishin fasfo din zuwa Ilesa, gwamnan ya yi nuni da cewa hakan zai saukaka matsalolin da jama’a ke fama da su a lokacin da ake yin fasfo.
Adeleke ya yabawa Ministan, “Ka sanya Osun alfahari a matsayin Minista kamar yadda ka kawo ayyukan raya kasa da dama a Osun kuma ina rokon Allah ya kara taimakonka.”
Tun da farko a nasa jawabin, ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ya bayyana cewa fasfo na daya daga cikin muhimman takardu da ya kamata kowa ya mallaka tun da yake hanya ce ta tantancewa baya ga tafiya kasashen waje.
Aregbesola ya kuma kara da cewa yana daya daga cikin wajabcin zama dan kasa na ‘yan Najeriya.
Tsohon Gwamnan na Osun ya jajirce cewa, an kawar da koma bayan fasfo, inda ya kara da cewa a yanzu ana iya sarrafa fasfo cikin makonni 3.