Hukumar hana fasaƙwaurin kayayyaki ta Kwastam, ta kama maganin tari na codeine mai kimar Naira miliyan 212 da kuma maganin ƙarfin maza.
Kwantirola na yankin Apapa da ke Jihar Legas, Hammi Swomen, ya ce, sun kama kwantena ɗauke da katan 2,875 na maganin tarin da kuma katan 383 na ƙwayar da ke ƙarfin jima’i, waɗanda aka bayyana da wani suna na daban.
Haka nan, akwai katan 99 na na’urar niƙa abubuwa a cikin kwantenar.
Ya ce, “Abin da aka ce an ɗauko shi ne flas na abinci, amma kamar yadda kuke gani a bayana abubuwa ne daban kwatakwata,” a cewarsa.
BCC ta rawaito cewa, wannan ba ƙarya ba ce kawai, an shigo da haramtattun abubuwa. In ji Hammi.