fidelitybank

Kwastam ta kama Shinkafa mai ɗauke da guba ƴar Indiya

Date:

Hukumar Kwastam a Ikeja, a ranar Alhamis, ta ce, ta kama buhunan shinkafa ‘yar waje mai guba da aka shigo da su daga kasar Indiya, aka kuma yi safarar su ta Jamhuriyar Benin zuwa cikin kasar.

Da yake jawabi yayin ganawa da manema labarai a Legas, mukaddashin Kwanturola na FOU, shiyyar A, Hussein Ejibunu, ya ce, hukumar kula da ingancin magunguna ta kasa (NAFDAC) ta yi gwajin shinkafar kasar waje, inda ta tabbatar da cewa, shinkafar na dauke da dalma (a). soft heavy toxic malleable metallic element), wanda ke da guba ga lafiyar jama’a, ko da yake ya ce, an kama mutane 12 da ake zargi da hannu wajen kame daban-daban.

Bayan mun kama shinkafar da aka yi fasakwaurin ne, sai muka kira hukumar NAFDAC, domin gudanar da binciken dakin gwaje-gwaje, an tattaro cewa, shinkafar mai suna SIMBA ta kunshi sinadarin gubar. Abun da ya kunsa yana da guba ga jiki kuma yana da hadari ga lafiyar jama’a”, in ji shi.

Ejibunu ya kuma ce, rundunar ta kama PMS lita 55,800, bale 73 na rigunan da aka yi amfani da su, firji guda 82, na’urar kwampressor guda 104, bales na sabbin masaku 143, tayoyin da aka yi amfani da su guda 1,264, katan 156 na daskararrun kaji guda 7,960. sababbin takalma da sauransu.

Ya yi bayanin cewa, bisa tsarin gwamnatin tarayya na karfafa noman shinkafa a cikin gida a kan shigo da shinkafar da ake shigowa da su waje, hukumar ta Kwastam, ta kama buhunan shinkafa 7,259 (na kilo 50 kowanne) wanda kwatankwacin manyan motoci sama da goma sha biyu (12) ne. .

tribune news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp