fidelitybank

Kwastam ta kama sassan Jakuna na Naira biliyan 1.23 da za a fitar waje

Date:

Hukumar kwastam ta kwace tarin mazakutar jakuna da kuma ƙayoyin kifi da kuɗinsu ya kai Naira biliyan 1.23 a filin jirgin saman Legas wanda aka yi niyyar fita da su zuwa China da Hong Kong.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Alhamis, ta ce ba ya ga al’aurar jakunan ta kuma samu nasarar kama wasu haramtattun kayayyakin.

Kwamandan hukumar a jihar, Muhammed Yusuf, ya bayyana cewa wani ɗan ƙasar China ne ya ɗauko al’aurar jakunan na maza daga garin Abakaliki na jihar Ebonyi da nufin tafiya da su ƙasarsa ta asali.

“Jakuna na cikin dabbobi da ke barazanar karewa, sai muka fara tunanin dalilin da ya sa suka fito daga wannan bangaren,” in ji sanarwar hukumar.

Ya ce idan ba a ɗauki matakin da ya kamata ba jakuna za su kare a faɗin ƙasa. Hukumar ta ce an kama ɗan Chinar kuma ana ci gaba da bincike.

Game da ƙayoyin kifin da aka kama kuwa, hukumar ta ce ana ci gaba da bincike domin gamo daga wajen da aka kawo su saboda ganin cewa ba bu isassun nau’in kifin shark a tekun Najeriya.

A ɗaya ɓangaren, hukumar ta ce daga watan Janairu zuwa Yulin 2023, ta samu kuɗaɗen shiga da suka kai N47.24bn.

nnn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp