fidelitybank

Kwastam ta kama mota ɗauke da sinadaran haɗa bam

Date:

Hukumar Kwastam ta kasa, reshen yankin Seme, ta kama wata mota da ake zargin tana ɗauke da kayan haɗa bam (IED).

Wannan na ƙunshe ne a wani bidiyo da hukumar ta wallafa a shafinta na X, inda jami’anta ke binciken motar da aka kama a kan titin Lagos zuwa Badagry.

An gano cikin motar akwai kwanso guda shida na ma’adani mai launin azurfa mai ɗauke da guba mai ƙarfi da aka fi sani da corrosive mercury — wanda ake kyautata zaton ana amfani da shi wajen haɗa abubuwan fashewa.

Shugaban Kwastam na yankin, Kwanturola Ben Oramalugu, ya ce an kama mutum ɗaya da ake zargin yana da alaƙa da motar.

Ya bayyana cewa nasarar kama motar na nuna yadda Kwastam ke cikin shiri da kulawa wajen kare tsaron kasa.

Oramalugu ya kara da cewa wannan aiki na cikin matakan da Kwastam ke dauka don dakile ayyukan fasa-kwauri da sauran laifuka a iyakokin Najeriya.

Baya ga motar da ake zargin tana ɗauke da kayan haɗa bam, hukumar ta kuma kama wasu kayayyaki da dama da suka saɓa wa doka.

Kayayyakin sun hada da kuɗaɗen ƙasashen waje daga Birtaniya da Kanada, da Amurka da darajarsu ta kai kusan naira miliyan tara, wanda hakan ya saɓa dokar harajin kaya na waje.

Sauran kayayyakin da aka kama sun hada da robar ganyen wiwi guda 553 da buhunan shinkafar waje 1,415 da jarkokin man fetur guda 750, da kuma magungunan da ba a yi rijistarsu ba.

Kwanturola Oramalugu ya ce hukumar za ta miƙa kayayyakin da aka kama ga hukumomin da suka dace domin gudanar da bincike tare da ɗaukar mataki, da gurfanar da wadanda ake zargi.

legit new

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Obi da El-Rufa’i za su koma jam’iyyar mu a hukumance – ADC

Sakataren yada labarai na rikon kwarya na jam’iyyar African...

Za mu tattauna da tarayyar Turai a kan Nukiliyarmu – Iran

Iran ta tabbatar cewa za ta gudanar da tattaunawa...

Mu na gargadin Isra’ila kan korar al’ummar Gaza daga yankin su – MDD

Hukumar kula da ayyukan jin-ƙai ta Majalisar Ɗinkin Duniya...

Rikici ya kuma balle a Syria

Ƙungiyoyin kare haƙƙin dan'adam sun ce, wani sabon rikici...

Tsofaffin ‘Yansanda na da ‘yancin yin zanga-zanga – A Cewar Amnesty

Ƙungiyar Amnesty International ta ce tsofaffin ƴansandan Najeriya girmamawa...

Buhari ya yi wa Najeriya hidimar da ba za a manta da shi ba – António Guterres

Babban Sakatare na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) António Guterres...

Binani ta koma jam’iyyar haɗaka ta ADC

'Yartakarar gwamnan jihar Adamawa a zaɓen 2023, Sanata Aishatu...

A Talata zan koma aiki na a majalisa – Natasha

Yar majalisar Dattawa, Sanata Natasha Akpoti, ta ci alwashin...

An sake mayar da yan Najeriya 294 gida daga Nijar

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya Nema ta...

An gano motoci 35 da aka sace a wata shida

Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa a Najeriya ta ce...

Shugaban Laberiya ya je ta’aziyyar Buhari a Monrovia

Shugaban Ƙsaar Laberiya Joseph Nyuma Boakai ya kai ziyarar...

Rundunar Yansandan Kaduna ta hana gangamin goyon bayan Peter Obi

Rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar Kaduna ta hana gudanar...
X whatsapp