Hukumar Kwastam ta kwace litar man fetur 150,950, wanda kudinsu ya kai Naira 105,965,391 a cikin mako guda.
Kwanturolan Janar na hukumar ta kasa, Bashir Adewale Adeniyi ne ya bayyana hakan, yayin ganawa da manema labarai a jihar Adamawa.
Ya ce a karkashin wani aiki na musamman na Oepration Whirl Wind da aka kaddamar makonni biyu da suka gabata, hukumar ta kama lita 150,950 da kudinsu ya kai Naira 105,965,391.
Ya kuma ce fasa-kwaurin man fetur ya zama ruwan dare, wanda ake kai su kasashen da ke makwabtakan Jamhuriyar Benin da kuma Kamaru.