Hukumar Kwastam ta kama wata kwantena mai tsawon mita 40 da ke dauke da makamai daban-daban da kwantena tara makare da codeine a tashar jirgin ruwa ta Onne da ke jihar Ribas.
Babban Kwanturolan Hukumar Kwastam, Bashir Adewale Adeniyi, wanda ya gabatar da makaman da aka kama ga manema labarai a garin Onne na Jihar Ribas, a ranar Litinin din da ta gabata, ya ce an shigo da makaman ne cikin Kasar daga Turkiyya.
Ya ce an boye makaman da magungunan ne a cikin tufafin da aka yi amfani da su.