Hukumar hana fasa kwauri ta kasa reshen Adamawa da Taraba, ta sanar da kama wasu haramtattun kayayyaki har sau 15 da kudinsu ya kai N13, 352,100.
Ayyukan da suka haifar da kamun an gudanar da su ne daga farkon watan jiya zuwa yau.
Kayayyakin da aka kama sun hada da lita 16,675 na man fetur da aka jibge a cikin jarka da shinkafar waje.
Shugaban Hukumar NCS na yankin Adamawa/Taraba, Salisu Kazaure Abdullahi, wanda ya yi wa manema labarai jawabi kan kamun, ya ce ana ci gaba da safarar kayayyakin man fetur daga kasar nan duk da cire tallafin man fetur.
“Wannan ya faru ne sakamakon hauhawar bukatar man fetur da kuma tsadar kayayyaki a kasashe makwabta kamar Kamaru, Togo, da Jamhuriyar Benin,” in ji jami’in kwastam na yankin.
Ya ce kungiyoyin masu safarar man fetur na da taurin kai kuma suna da dimbin albarkatu kuma saboda suna samun makudan kudade wajen safarar kayan da ake shigowa da su kasar nan, suna kokarin ci gaba da gudanar da sana’ar ta haramtacciyar hanya ko ta halin kaka.
Ya kuma ba da tabbacin cewa hukumar ta NCS tana ci gaba da duba dabarunta tare da murkushe masu fasa kwauri.
“Muna so mu gaya wa masu fasa-kwauri ba tare da wata shakka ba cewa idan suka canza salo, za mu canza namu kuma gaskiya za ta yi nasara a kan karya,” in ji shi.