fidelitybank

Kwastam ta fara sayar da shinkafa buhu Naira dubu 10

Date:

Hukumar hana fasa kwauri ta Najeriya kwastom ta fara sayar da shinkafa kan farashin mga ‘yan kasar.

Matakin na daga cikin ayyukan rage radadin tattalin arzikin da ‘yan NAjeriya ke fuskanta

Mai magana da yawun hukumar Abdullahi Maiwada ya shaida wa BBC cewa shinkafar da hukumar ke sayarwa, shinkafa ce da jami’an hukumar suka kama a lokacin da aka shigar da ita kasar ba bisa ka’ida ba.

Ya ce hukumar ta kai shinkafar kotu inda suka samu sahalewar kotu domin sayar da ita ga talakawan kasar.

Abdullahi Maiwada ya ce an fara sayar da sayar da shinfara ne a yau Juma’a a jihar Legas, a matsayin gwaji kafin daga baya hukumar ta fadada aikin zuwa sauran jihohin kasar da take da irin wadannan kaya da ta kama.

Kakakin hukumar ya ce suna sayar da buhu mai nauyin kilogiram 25 na shinkafar a kan kudi naira 10,000.

Matakan da hukumar ke bi wajen sayar da shinkafar

Abdullahi Maiwada ya ce hukumar na bin wasu matakai na tantancewa kafin ta sayar da shinkafar ga al’umma kamar haka.

  • Amfani da NIN – Ya ce hukumar na amfani da lambar da ke jikin katin dan kasa ta NIN wajen tantance mutanen da take sayar wa shinkafar, don haka dole sai wanda ke da lambar NIN zai samu damar sayenta.
  • Mutanen da ke kusa da inda hukumar ta kama kaya– Abdullahi Maiwada ya ce hukumar na sayar da shinkafar ne kawai ga mutanen da ke kusa da inda ta kama shinkafar, ”don haka duk mutmin da ya zo daga nesa ba zai samu sayen shinkfara ba”, in ji shi.
  • Masu sana’ar hannu – Kakakin hukumar Kwastam din ya ce daga cikin rukunin mutanen da hukumar ke sayar wa shinkafar su ne masu sana’ar hannu. Ya ce an yi hakan ne domin tallafa musu wajen bunkasa sana’o’insu.
  • Malaman makaranta – Hukumar ta ce malaman makaranta na daga cikin rukunin mutanen da za su amfana da sayen da sayen shinkafar da hukumar kwastam ke sayarwa.
  • Masu sharar titi – Abdullahi Maiwada ya kara da cewa su ma mutanen da ke sharar titi na daga cikin rukunin mutae da hukumar ba domin sayar musu da shinkafar.
  • Mutanen da suka fi tsananin bukata – Kakakin hukumar ya shaida wa BBC cewa dama makasudin sayar da shinkafar shi ne rage wa al’immar radadin tsadar rayuwa da ‘;yan kasar ke fuskanta, don haka ya ce suka fi bayar da fifiko kan mutanen da ke cikin tsananin bukata.
  • Mata – Wasu rukunin mutanen da za su amfana da shinkafar kwastam din mai cike da rahusa su ne mata, musamman marasa karfi, wadanda ke rike da kananan yara.
  • Kungiyoyin addini – Kungiyoyin addini na daga cikin al’umomin da za su amfana da wannan sayar da shinkafa da hukumar kwastam ke yi, kamar yadda hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook.

Hukumar ta kuma gargadi ‘yan kasar da ke da aniyar sayar da shinkafar ga ‘yan kasuwa, da su guji yin hakan.

Abdullahi Maiwada ya ce duk wanda ya yi haka zai fuskanci fushin hukumar, sannan kuma ya ce hukumar za rika sanya idanu a kasuwanni domin ganin ko ‘yan kasuwa za su sayi shinkafar domin sayarwa.

nigeria news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp