Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) ta ceto wata yarinya daga jihar Oyo.
An ceto yarinyar mai shekaru 17 a ranar 26 ga watan Nuwamba a birnin Kebbi a lokacin da ake zargin ta dauki hanyarta ta zuwa kasar Libya.
Tana tafiya ita kadai a inda aka kama ta, a wani wuri a karamar hukumar Yauri.
Kwanturolan hukumar NIS a Kebbi, Rabi Bashir-Nuhu ta shaida wa manema labarai cewa yarinyar ta yi ikirarin tafiya Sakkwato ne.
“Muna da yakinin cewa ana safarar ta ne don zuwa Libya domin a yi amfani da ita wajen yin aikin kwadago, karuwanci ko kuma girbin gabobi”, kamar yadda NAN ta ruwaito.
Matashiyar ta shaida wa jami’an shige da fice cewa mahaifiyarta ta aike ta domin ta gana da wata Zainab a Sakkwato.
Amma matar ta yi ikirarin cewa ba ta da lafiya lokacin da aka gayyace ta ofishin NIS da ke Kebbi.
“Wannan ya sa muka yi imanin cewa yarinyar ta kasance cikin fataucinsu. Ba ta da takarda ko da ko kwabo,” Bashir-Nuhu ya kara da cewa.
Kwamandan hukumar hana safarar mutane ta kasa (NAPTIP), Misbahu Iyya-Kaura, wanda ya tarbi yarinyar ya ce za a binciki lamarin.