fidelitybank

Kwastam sun harbe mutum biyu a Jigawa

Date:

Hukumar Kwastam ta kasa NCS a wani atisayen kan iyaka ta sake bindige wasu mutane biyu, bisa yunkurin kawo musu cikas a aikinsu a karamar hukumar Ringim ta jihar Jigawa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan DSP Lawan Shiisu Adam ya tabbatar wa DAILY POST faruwar lamarin.

Ya ce lamarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar a kauyen Gidan Lage yayin da wasu fusatattun matasa suka yi yunkurin hana rundunar hadin guiwa da jami’an tsaron kan iyaka gudanar da aikin a yankin.

Ya ce a yayin gudanar da ayyukan an kwato buhunan shinkafar kasashen waje da dama.

Shiisu ya bayyana cewa matasan kauyen sun taru sun yi yunkurin hana jami’an gudanar da aikin.

Ya bayyana cewa a sakamakon haka jami’an sun harba wasu harsasai kan masu zanga-zangar kuma an harbe mutane biyu kuma suka samu raunuka.

Shiisu ya ce ‘yan sanda sun garzaya wurin da laifin ya faru inda suka kai wadanda abin ya shafa asibitin Gabasawa da ke jihar Kano domin kula da lafiyarsu.

Wannan na zuwa ne kwanaki bayan da jami’an kwastam da ke aikin atisayen kan iyaka a kan iyakar Nijar da Najeriya sun haddasa fashewar motar dakob iskar gas da ta lalata gidaje, da shaguna da raunata da dama a karamar hukumar Babura.

vanguard (nigeria)

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp