Hukumar kula da aikin ‘yan sanda a Najeriya, ta koka kan abin da ta kira rashin nuna ƙwarewa da ƴan sandan sarauniya ko kuma ‘yan sandan sa-kai ke nunawa, a ƙoƙarin da suke yi wajen tallafa wa tsaron al’umma.
Hukumar ta bayyana haka ne cikin wata sanarwar da shugaban yaɗa labaranta, Ikechukwu Ani ya fitar, inda ta nemi a canza wa ‘yan sandan sarauniya kaki ko inifom, ko kuma a rushe ayyukansu a jihohi matuƙar ba za a riƙa biyan su haƙƙoƙin aiki da kuma kula da su ba.
A cewar hukumar, akwai hatsari a bai wa ‘yan sandan sarauniya bindiga, kuma a ba su lasisin samar da tsaro da tabbatar da doka da oda a jihohi da yankunan ƙasar, ba tare da biyan su albashi ba.
Hukumar ta gano cewa ‘yan sandan sarauniya suna karɓar cin hanci a hannun ƴan Najeriya ta hanyar tilastawa da kuma tsoratarwa.
Ta kuma ce hankalinta bai kwanta ba da tsarin rundunar ‘yan sandan sarauniya ta musamman da kuma yadda take tafiyar da ayyukanta a faɗin Najeriya.
Ta ce tuni ta tuntuɓi babban sufeton ƴan sandan Najeriya game da buƙatar sauya fasalin rundunar da kuma ayyukanta.
A cewar hukumar, sauya musu kaki, zai taimaka sosai wajen sa ido kan ayyukansu, da ma sauran jami’an ƴan sanda tare da tsame rundunar ƴan sandan Najeriya daga zargin da take sha saboda rashin ɗa’ar ‘yan sandan sarauniya.
An ruwaito Shugaban hukumar ta PSC, Solomon Arase wanda tsohon jami’in ɗan sanda ne yana cewa hukumarsa za ta yi aiki tare da shugabancin rundunar ƴan sanda ta ƙasar domin tsaftace ayyukan ‘yan sandan sarauniya.


