Bulaliyar Majalisar Dattawa, Orji Kalu, ya ce, Rabi’u Kwankwaso, zai iya zama wanda zai lashe zaben shugaban kasa a 2023, idan har jam’iyyar APC mai mulki ta kasa tsayar da tikitin takarar ta na shiyyar Arewa maso Gabas ko kuma Kudu maso Gabas.
PlatinumPost ta rawaito cewa, Kwankwaso tsohon gwamnan jihar Kano, ya sauya sheka daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa New Nigeria People’s Party NNPP.
Amma Kalu, wanda kuma tsohon gwamnan jihar Abia ne, ya ce, bai kamata a yi watsi da sauya shekar Kwankwaso zuwa NNPP tare da wasu fitattun ‘yan siyasa ba.
Ficewar manyan ‘yan takarar jam’iyyar zuwa New Nigeria People’s Party, NNPP, musamman a shiyyar Arewa-maso-Yamma, bai kamata a ce babbar jam’iyyarmu ta APC ta yi wasa da ita ba.