Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP), Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya nada Abdulmumini Jibrin da Ladipo Johnson a matsayin masu magana da yawun yakin neman zaben sa na 2023.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Ibrahim Adamu, mataimaki na musamman ga Kwankwaso ya fitar a Abuja ranar Alhamis.
A cewar sanarwar an nada Jibrin da Johnson ne saboda kwarewa da jajircewarsu.
“An zabo su biyun ne saboda kwarewarsu a fannin sadarwa, da jajircewarsu ga jam’iyyar NNPP, babbar hanyar sadarwar da suke da ita, da kuma imanin da suke da shi kan yakinin da muka yi na cewa sabuwar Najeriya mai kyau za ta yiwu idan muka yi aiki tare da gaskiya, haƙuri, iyawa, da imani.


