Wakilai ko daliget na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, daga kananan hukumomi 774 na fadin Najeriya sun tabbatar da tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Kwankwaso a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2023.
Jam’iyyar ta tsayar da tsohon gwamnan na Kano ne ba tare da hamayya ba a taron da ta gudanar ranar Laraba a Abuja, babban birnin kasar.
Yanzu ke nan, Kwankwaso zai fafata da Alhaji Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC da sauran ‘yan takarar shugaban kasa a zaben da za a yi a shekara mai zuwa.
Sanata Kwankwaso ya ce idan aka zabe shi a matsayin shugaban Najeriya zai kyautata harkokin ilimi da tsaro da ilimi da kuma share wa talakawa hawayensu.