Gabanin zaben 2023, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, Rabi’u Kwankwaso ya isa kasar Amurka domin tattaunawa da wasu jami’an gwamnati.
Tsohon gwamnan jihar Kano ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis da daddare.
Da yake raba hotunan zuwansa, dan takarar na NNPP ya rubuta cewa, “Na zo ne don ganawa da wasu manyan jami’an gwamnatin Amurka, a Washington DC”.
Sauran ‘yan takarar shugaban kasa da suka hada da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP, da Peter Obi na jam’iyyar Labour sun kasance a Amurka a kwanan baya.
Hakazalika, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, APC, Bola Tinubu, zai iya zuwa Amurka a mako mai zuwa domin neman goyon bayan zaben watan Fabrairu.