Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi wata ganawa da zaɓaɓɓen shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a birnin Paris.
Bayanai sun nuna cewa mutanen biyu sun shafe sa’o’i da dama suna tattaunawar.
Wata majiya da ba ta son a ambace ta, ta tabbatar wa BBC da ganawa a ƙasar Faransa.
Kwankwaso, wanda shi ne tsohon gwamnan jihar Kano ya zo na huɗu a cikin ƴan takarar shugaban ƙasa na 2023, inda ya samu ƙuri’u 1,496,687.
Bola Tinubu, wanda tsohon gwamnan jihar Legas ne kuma ɗaya daga cikin waɗanda ake wa kallon ƙwararru a siyasar Najeriya, har yanzu bai yi bayani dalla-dalla kan yadda gwamnatinsa za ta kasance ba.
A halin da ake ciki, zaɓaɓɓen shugaban ƙasar, Bola Tinubu na ƙoƙari ne wajen ganin ya shirya yadda zai karɓi mulki ranar 29 ga watan Mayu.
A ranar Laraba 10 ga watan Mayu ne zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ya bayyana cewa zai tafi wata ziyarar aiki a ƙasashen Turai.