Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya caccaki jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kan yadda ta tsayar da fom din ta na neman tsayawa takarar shugaban kasa a kan Naira miliyan 100.
Sanata Kwankwaso, wanda shi ne jigon jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP na kasa, ya kuma bukaci ‘yan Nijeriya da su hada kai da jam’iyyar su karbi fom din tsayawa takarar fidda gwanin jam’iyyar, yana mai cewa an yi wa fom din rahusa ne ga masu sha’awar shiga jam’iyyar.
Wannan dai na zuwa ne a karshen mako da jam’iyyar ta gudanar da taron majalisar zartarwa ta kasa, NEC, a Abuja.
Da yake zantawa da manema labarai a wurin taron, tsohon gwamnan jihar Kano, ya tabbatar wa magoya bayan jam’iyyar NNPP cewa jam’iyyar za ta samu gagarumar nasara a babban zaben shekara mai zuwa.
Ya ce, ba kamar yadda jam’iyyar APC ta tsayar da fom din takarar shugaban kasa a kan Naira miliyan 100 ba, jam’iyyar NNPP ta yi na ta fom din da arha.