A yayin da kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Kano ke shirin bayyana hukuncin da za ta yanke a karar da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta shigar kan jam’iyyar NNPP da aka zabi Abba Kabir Yusuf, magoya bayan Kwankwasiyya karkashin jagorancin Rabiu Musa Kwankwaso, sun yi ta addu’o’i na musamman na kin karbe musu zabensu.
Addu’o’in na musamman da aka gudanar a Filin Mahaha, ya samu halartar Gwamna Abba Kabir Yusuf, Shugaban Jam’iyyar NNPP na kasa, Dr Rabi’u Musa Kwankwaso, Mataimakin Gwamna Aminu Abdussalam, Sakataren Gwamnati na Jiha, Dr Baffa Bichi, da sauran manyan jami’an gwamnatin tarayya.
A yayin addu’ar ta musamman, Imam Sani Hashir ya ce, “Mun yi addu’a ne a yau domin nuna godiyarmu ga Allah da ya ba mu nasara a zaben 2023, ya kuma kiyaye al’ummarmu, ya kuma tabbatar da zaman lafiya a jiharmu, ya kuma tabbatar da zaman lafiya a kasarmu.
“A jihar Kano a yau, Allah ya albarkace mu da shugabanni da suka fara sauya fasalin jihar inda ruwan bututun ya fara kwararowa a dukkan sassan jihar, an gyara fitulun tituna da gyaran asibitoci da kayan aiki.
“Ya kuma lura cewa jihar Kano na biyan kudin rijistar dalibai marasa galihu na jami’ar Bayero sama da dubu bakwai yayin da ake gyaran tituna da juji suna bacewa.
“Duk da haka, duk da wannan kokarin da gwamnati mai ci ta yi kafin cikar kwanaki dari na kan karagar mulki, makiyan jama’a na yin makirci da shirin yiwa shugabanninmu zagon kasa.”


