An shirya tsaf domin bayyana tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso a matsayin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a 2023.
Shugaban jam’iyyar NNPP na kasa kuma wanda ya kafa ta, Dokta Boniface Aniebonam ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a ranar Juma’a.
A cewarsa, babban taron jam’iyyar na musamman da aka shirya yi a ranar 8 ga watan Yuni a Abuja, za a yi amfani da shi wajen tabbatar da takarar Kwankwaso, domin shi kadai ne dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP wanda ke nufin za a dawo da shi ba tare da hamayya ba.
Aniebonam yayin da yake yaba halayen Kwankwaso ya bayyana tsohon ministan tsaro a matsayin bawan Allah wanda zai iya magance yawancin matsalolin Najeriya.