Wani jigo a jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, Buba Galadima, ya yi watsi da ikirarin cewa, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben da ya gabata, Rabiu Kwankwaso, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress, APC.
Galadima ya ce har yanzu Kwankwaso bai sanar da NNPP cewa zai koma APC ba.
Da yake magana da gidan Talabijin na Channels, jigon na NNPP, ya bayyana cewa Kwankwaso a shirye yake ya yi aiki da shugaban kasa Bola Tinubu.
A cewar Galadima: “Kwankwaso bai fadawa kowa cewa zai koma APC ba; mutane suna magana kawai, amma abin da muke da shi a baya shine mai nasara ya dauki duka. Idan Tinubu yana kira da a kafa gwamnatin hadin kan kasa, ba wani mummunan abu ba ne.”
Ana ganin Kwankwaso a kusa da Tinubu tun bayan da ya lashe zaben shugaban kasa a watan Fabrairu.
Akwai ra’ayin cewa Tinubu zai iya ba Kwankwaso mukamin siyasa.