An dinke barakar da ta kunno kai a tsakanin jaruman fim din Hausa na Kannywood a cikin makon nan, saboda wasu maganganu na tozarci da Ladin Cima ta kwance musu zani a kasuwa.
An samu sabani tsakanin jaruman Kannywood kan batun yadda furodusoshi ke biyan kudi kan fina-finai.
A yanzu dai Naziru Sarkin Waka ya ce, an zauna da jaruman, an tattauna da juna an kuma samu mafita daga karshe.
Tun bayan da aka sha fama a tsakani, tare da luguden maganganu da cece-kuce a masana’antar Kannywood a makon nan, an samu dakyar kura ta lafa.
Cece-kucen da ya dauki kwanaki biyu ana fama ya faro, tun lokacin da BBC ta yi hira da wata dattijuwar jarumar fim, inda ta fadi yawan kudin da ake biyan jarumai.