Kwamitin zartaswa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a shiyyar Arewa maso Gabas, sun tabbatar da korar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2023, Rabi’u Musa Kwankwaso.
An bayyana hakan ne a cikin sanarwar da aka fitar a karshen taron zartarwa da masu ruwa da tsaki na yankin Arewa maso Gabas da aka gudanar a Bauchi ranar Juma’a.
Bugu da kari, jam’iyyar NNPP ta arewa maso gabas ta nuna rashin gamsuwarta da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke na tsige gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf.
Mataimakin shugaban jam’iyyar NNPP na kasa ta Arewa, Dakta Babayo Liman, a cikin sanarwar da ya karanta wa manema labarai, ya yi alkawarin ci gaba da marawa gwamnan baya tare da yin kira ga hadin kan ‘ya’yan NNPP a fadin kasar nan.
Taron ya kuma tabbatar da rusa kwamitin ayyuka na kasa a karkashin jagorancin Abba Kawu Ali na jam’iyyar NNPP.
Kwamitin zartarwa na NNPP da masu ruwa da tsaki a shiyyar Arewa maso Gabas sun amince da kada kuri’ar amincewa da wanda ya kafa kuma memba na kwamitin amintattu, Dokta Boniface Aniebonan.
Taron ya sake tabbatar da zaben Dr. Tope Aluko a matsayin shugaban kwamitin amintattu da Engr. Mohammed Babayo Abdullahi a matsayin Sakatare.
An kuma tabbatar da nadin sabuwar hukumar ta NWC karkashin jagorancin Dr Agbo Major.


