Kwamitin shiga tsakani na Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Afirka ta Yamma (Ecowas) na kan hanyar koma wa Jamhuriyar Nijar, a ƙoƙarin ganin an shawo kan dambarwar siyasar ƙasar ta hanyar lumana.
Juyin mulkin da dakarun tsaron fadar shugaban ƙasa suka yi wa Shugaba Bazoum Mohamed ranar 26 ga watan Yuli, ya janyo zazzafan mataki daga Ecowas.
Ana sa ran, kwamitin zai tashi da safiyar Asabar daga Abuja zuwa Yamai, babban birnin Nijar.
Matakin na zuwa ne kwana ɗaya, bayan Ecowas ta ce taron manyan hafsoshinta na kwana biyu a birnin Accra, ya saka ranar kai yaƙi Nijar. In ji BBC.
Kwamishinan harkokin siyasa na Ecowas, Ambasada Abdel-Fatau Musah ya ambato su, suna cewa: “Mun shirya shiga a duk lokacin da aka ba mu umarni”.
Amma dai, Ecowas ta jaddada cewa duk da wancan mataki ƙofofin sulhunta rikici ta hanyar diflomasiyya za su ci gaba da kasancewa a buɗe.
Ta ce za ta sake aika wasu jami’an shiga tsakani zuwa Nijar nan da ‘yan kwanaki.
A baya, wa’adin Ecowas da ƙoƙarin diflomasiyya ba su iya tanƙwara sojoji masu mulki a Nijar ba wajen mayar da hamɓararren Shugaba Bazoum Mohamed kan karagar mulki.
Wata majiya a cikin kwamitin diflomasiyyar na Ecowas, ƙarƙashin jagorancin Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya), ta ce saɓanin ziyarar farko, a wannan karo suna sa ran samun kyakkyawar tarba daga shugabannin mulkin sojan Nijar.
A karon farko, rahotanni sun ce kwamitin Abdulsalami Abubakar bai samu kyakkyawar tarba a Yamai ba, hasali ma jami’an diflomasiyyar ba su iya shiga gari ba, daga filin jirgin saman Diori Hamani.
Babu masaniya a kan irin tuntuɓa ta bayan fage da aka ci gaba da yi kan rikicin siyasar na Nijar kafin wannan lokaci, amma majiya daga kwamitin ta ce suna da ƙwarin gwiwa a wannan karo za su gana da Janar Abdourahamane Tchiani.
Ta ce: “Duk da yake Ecowas ta cimma waccan matsaya a birnin Accra, amma har yanzu babu wanda yake son yin yaƙi.”