Kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya zai tattauna yau Talata kan makomar sauran mutanen da ake ci gaba da garkuwa da su a Gaza.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu rahotanni ke cewa Isra’ila na nazarin mamaye yankin Gaza baki ɗaya.
Wakiliyar BBC ta ce an kira taron na Majalisar Ɗinkin Duniya bayan mayaƙan Falasɗinawa sun fitar da wani bidiyo da ke nuna biyu daga cikin waɗanda suke tsare da su cikin mawuyacin hali.
Iyalan mutanen sun bayyana damuwa kan bayanan da ke nuna cewa Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu na shirin mamaye ɗaukacin yankin Gaza ciki har da wuraren da ake tsare da mutanen.
Sai dai wasu rahotanni na cewa wasu shugabannin sojin Isra’ila sun bayyana adawa da matakin, a yayin da halin jin ƙai a Gaza ya kasance mai matuƙar muni.