Kwamitin majalisar dokokin Birtaniya ya soki kudurin gwamnatin kasar kan masu neman mafaka.
Kwamitin ya ce babu wata kwakkwarar hujja da ke nuna cewa tura masu neman mafaka zuwa Rwanda zai tsayar da kwararar ‘yan ci rani zuwa cikin Burtaniya.
Gwmanatin Burtaniya dai ta sha nanata cewa shirin nata zai dakatar da kwararar bakin haure zuwa kasar ta hanyar tafiya cikin teku mai cike da hatsari.
A watan Afirilu ne dai gwamnatin kasar ta cimma yarjejeniya da kasar Rwanda domin tura ‘yan ci-ranin zuwa kasar. In ji BBC.
To sai dai kawo yanzu ba a fara kwashe su ba saboda rashin kammala aiwatar da yarjejeniyar.